Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yankin Chongli na birnin Zhangjiakou dake lardin Hebei ya samu ci gaba cikin sauri
2020-09-13 20:32:24        cri

A ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2015, birnin Beijing da birnin Zhangjjiakou na lardin Hebei na kasar Sin sun samu damar shirya gasar wasannin Olympic na yanayin hunturu na shekarar 2022 cikin hadin gwiwa, an kuma zabi yankin Chongli na birnin Zhangjiakou da ya kasance babban filin wasannin kankara mai laushi ta gasar wasannin Olympic, lamarin da ya samar da damar samun ci gaba ga yankin Chongli, ya zuwa watan Mayun shekarar 2019, yankin ya kubutar da kansa daga kangin talauci, har ya samu ci gaba cikin sauri.

Kowace shekara, yankin Chongli yana cikin yanayin hunturu har tsawon kwanaki 150, wato ana iya yin wasa kan kankara mai laushi a cikin wadannan kwanakin, don haka tun daga shekarar 1996, an fara wasan skiing a tsakanin duwatsu a yankin, inda ake da arzikin kankara mai inganci, kawo yanzu gaba daya akwai filayen wasan kankara na skiing a tsakanin duwatsu guda 7 a yankin, inda ake samar da guraben aikin yi kusan dubu 30, wato kashi daya bisa hudu na mazauna yankin suna yin aikin dake da nasaba da wasan motsa jiki.

Ci gaban yankin yana jawo hankalin matasa inda suke sha'awar koma garin, misali Li Jianjiang, mai shekaru 34 da haihuwa wanda ya koyi ilmin na'urar kwanfuta a jami'a ya taba yin aiki a birnin Beijing a shekarar 2005, amma ya koma garin dake yankin Chongli a shekarar 2015, yanzu haka yana kula da fasahar sadarwa a garin.

Li Jianjiang ya gaya mana cewa, "Yanzu ko wace rana ina zaman rayuwa tare da yarana da iyayena, ni ma ina taka rawa kan ci gaban garina, ina jin dadi matuka."

Shugaban yankin Chongli Zhao Zan ya bayyana cewa, "Kowa da kowa suna yin kokari matuka domin kyautata rayuwarsu."(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China