Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping da malamansa
2020-09-10 20:12:55        cri

A yayin da ake taya murnar bikin malamai na 36 a kasar Sin, babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya isar da gaisuwa da fatan alheri ga daukacin malaman makarantun fadin kasar, inda ya jaddada cewa, ya zama wajibi a martaba sana'ar ba da ilmi a fadin kasar.

Hakika a cikin shekaru sama da goma da suka gabata, har kullum shi kansa babban sakatare Xi, yana martaba malaman makaranta, kuma ya mai da hankali kan aikin ba da ilmi matuka, a ko da yaushe yana nunawa malamansa godiya, saboda sun taba ba shi ilmi.

Xi ya taba yin tattaunawa da malamai, da dalibai na jami'ar horas da malamai ta Beijing, a gabannin bikin ranar malamai na shekarar 2014, inda ya bayyana cewa, "Malaman da suka taba koyar da ni darussa suna da yawa, har yanzu ban manta da su ba, saboda sun koyar da ni ilmomi, sun kuma koyar da ni dabarun zaman rayuwa, alal hakika na amfana sosai."

A shekarun 1960, Xi ya taba yin karatu a makarantar Bayi dake nan birnin Beijing, a ranar 9 ga watan Satumban shekarar 2016, Xi ya koma makarantar domin ganawa da malamai da dalibai dake makarantar, inda ya gaishe da malaman da suka koyar da shi, kamar su Chen Zhonghan, da Chen Qiuying da sauransu, wadanda shekarun haihuwarsu sun riga sun zarta saba'in, amma ba su manta abubuwan da suka faru kafin shekaru sama da goma da suka gabata ba.

Bayan da Xi ya kammala karatu a makarantar Bayi, sai ya je kauyen Liangjiahe na birnin Yan'an dake lardin Shaanxi domin aiki a can, amma a cikin wadannan shekaru sama da goma da suka wuce, Xi bai taba mantawa da makarantar Bayi da malaman da suka koyar da shi ba, idan a duk lokacin da ya komo Beijing, ya kan tafi makarantar domin gaida malamansa.

Aikin ba da ilmi yana shafar makomar kasa, malaman makaranta suna koyar da ilmomi da tunani, haka kuma suna kyautata hallayar dalibai. Tun bayan babban taron wakilan JKS karo na 18 a shekarar 2012, sai babban sakatare Xi ya dukufa wajen ingiza aikin ba da ilmi a kasar Sin, ta hanyar martaba malaman makaranta, haka daliban kasar Sin da yawansu ya kai sama da miliyan 100 ke kokarin bautawa kasarsu, ta hanyar yin amfani da ilmomin da suka koya a makaranta. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China