Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An zuba jarin dala biliyan 88 a taron dandalin masana'antun kasa da kasa
2020-09-13 16:24:32        cri

Sama da ayyuka 600 wadanda jarinsu ya kai kudin Sin yuan biliyan 600, kwatankwacin dala biliyan 87.7 aka rattaba hannu kansu a ranar Asabar a yayin taron dandalin masana'antun sarrafa kayayyaki na kasa da kasa wanda aka gudanar ta kafar intanet a Hefei, babban birnin lardin Auhui dake gabashin kasar Sin.

Kasuwannin cikin gidan kasar Sin suna kara samun tagomashi, kana bunkasuwar fannin masana'antun sarrafa kayayyakin na kasar zai kara baiwa duniya muhimman damammakin ci gaban zuba jari, da kuma kara samar da kyakkyawar makomar bunkasuwar fannin zuba jari karkashin sabuwar manufar raya tattalin arziki ta ingiza ci gaban tattalin arziki ta hanyar cudanya a kasuwannin cikin gida da na ketare, mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin Wang Shouwen, shi ne ya bayyana hakan a lokacin bude taron dandalin tattalin arziki ta intanet na Jianghuai.

A karon farko, an gudanar da taron dandalin masana'antun na kasa da kasa ta kafar bidiyo sakamakon annobar COVID-19. Taron ya mayar da hankali ne kan batun inganta masana'antun sarrafa kayayyaki, da harkokin kasuwanci na zamani, da kuma yadda za a tafiyar da tsarin tattalin arzikin zamani da zai dace da bangaren tattalin arzikin samar da kayayyaki.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China