Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan ganawar shugabannin Sin da Jamus da Turai za ta ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya
2020-09-10 20:32:43        cri

A yau ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, ganawa ta kafar bidiyo da shugabannin kasar Sin, da Jamus da kuma Turai za su yi a ranar 14 ga wata, tana da muhimmanci matuka. A wannan rana, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai tattauna da shugabannin bangarorin Jamus, da Turai, kan huldar dake tsakanin Sin da Turai, da ma sauran batutuwan da suke jawo hankalinsu duka.

Jami'in ya yi nuni da cewa, bana ake cika shekaru 45 da kafa huldar diplomasiyyar Sin da kungiyar tarayyar Turai, ana kuma fatan ganawar da za su yi, za ta kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Turai, haka kuma za ta kare manufar bangarori daban daban, da gudanar da cinikayya maras shinge, da zaman lafiya da wadata a duniya, har ma ta ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya a yanayin da ake ciki yanzu.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China