Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tasirin ci gaban kasar Sin na zaman lafiya ne, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin
2019-12-05 20:26:50        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying, ta ce tasirin ci gaban kasar Sin na tattare ne da manufofin kasar na zaman lafiya da adalci. Hua ta bayyana hakan ne a Alhamis din nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa a nan birnin Beijing.

Tsokacin jami'ar na zuwa ne, bayan da Amurka ta bukaci kasashen Turai su ayyana Sin a matsayin barazana, to sai dai kuma hakan bai cimma ruwa ba, domin kuwa a taron kungiyar tsaro ta NATO da ya gudana jiya a birnin London, kasashen na Turai sun fitar da sanarwar da ta yi watsi da waccan bukata ta Amurka.

Daya daga jami'an kungiyar ta NATO da ba a bayyana sunan sa ba, ya ce mafi yawan kasashen Turai na ganin wannan roko na Amurka bai dace da bukatar al'ummunsu ba. Kungiyar NATO dai ta amince da matsayin kasar Sin na kasancewa kasar dake kara tasiri a duniya, amma hakan ba zai sa a dauke ta a matsayin abokiyar gaba ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China