![]() |
|
2020-09-03 21:34:02 cri |
A muhimmin jawabin da ya gabatar yayin taron, Xi Jinping, babban sakataren kwamitin koli na JKS kana shugaban kasa, ya yi nuni da cewa, Sinawa ba za su taba yarda wani ko wasu makiya su jirkita tarihin JKS ko wargaza yanayi da manufarta ba.
Haka kuma al'ummar Sinawa ba za su taba bari wani ko wasu makiya su lalata ko sauya tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin ba, kin amincewa ko bata manyan nasarorin da al'ummar Sinawa suka cimma wajen gina tsarin gurguzu. Sinawa ba za su taba yarda wani ko wasu makiya su yi kokarin hada gaba tsakanin JKS da al'ummar Sinawa ba. Al'ummar Sinawa ba za su taba amincewa da wani yunkuri da wani ko wasu makiya za su yi na tilastawa kasar Sin ra'ayinsu, ko sauya alkibar ci gaban kasar ko hana kokarin Sinawa na inganta rayuwarsu ba.
Al'ummar Sinawa, ba za su taba yarda da wani yunkuri daga wani ko wasu makiya na hana 'yancin al'ummar Sinawa na yin rayuwa da samun bunkasuwa cikin lumana ba, da yin musaya da hadin gwiwa tsakanin Sinawa da sauran al'ummun sauran kasashe, ko gwagwarmayar neman zaman lafiya da ci gaban bil-Adam. A duk tsawon jawabin da Xi jinping ya gabatar, mahalarta taron sun rika yi masa tafi. (Ibrahim Yaya)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China