![]() |
|
2020-09-03 09:50:17 cri |
A musayar sakonnin da suka yi da Putin domin bikin murnar cika shekaru 75 da samun nasarar kawo karshen WWII, Xi ya bayyana cewa, haka ma batun yake an cika shekaru 75 ke nan da samun nasarar Sinawa na kawo karshen yakin cin zali na harin Japanawa da yakin tarayyar Sabiya kan Japanawa wanda ya tabbatar da samun nasarar kawo karshen yakin cin zali a duniya.
A matsayinsu na kasashe masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Xi ya jaddada cewa Sin da Rasha dukkanninsu suna daukar muhimman nauyi dake bisa wuyansu domin tabbatar da zaman lafiya da cigaban duniya.
Ya ce a shirye yake ya yi aiki da Putin wajen amfani da nasarar cika shekaru 75 da samun nasarar kawo karshen nuna adawa da hare haren cin zali na duniya a matsayin wata muhimmiyar dama da za ta yiwa kasashensu jagoranci wajen zurfafa yin hadin gwiwa da juna.
Ya kuma jaddada cewa bangarorin biyu za su yi hadin gwiwa da kasa da kasa domin tabbatar da aiwatar da tsarin hadin gwiwar bangarori daban daban, da kuma gina tsarin makoma mai inganci ga dukkan bil adama, domin baiwa al'ummomi masu zuwa a nan gaba damar more rayuwa cikin yanayin zaman lafiya mai dorewa, da samar da tsaro na bai daya, da kuma kyakkyawar makoma gare su.(Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China