Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika CDC: An yi gwajin COVID-19 miliyan 11.8 a Afrika ya zuwa yanzu
2020-09-03 10:25:45        cri
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta sanar a ranar Laraba cewa, kasashe Afrika sun gudanar da gwajin cutar COVID-19 sama da miliyan 11.8 ya zuwa yanzu.

Africa CDC, kwararriyar hukumar lafiyar kungiyar tarayyar Afrika AU ta bayyana cewa, daga cikin gwaje gwajen cutar ta COVID-19 da aka gudanar a duk fadin Afrika wanda ya zarce miliyan 11.8 an samu kashi 10.7 bisa 100 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

A cewar hukumar dakile yaduwar cutuka ta nahiyar, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Afrika ya zuwa ranar Laraba ya kai kai 1,260,400, yayin da adadin mutanen da cutar ta hallaka ya kai 30,065.

Africa CDC ta ce, yawan mutanen da suka warke daga COVID-19 a nahiyar ya zarce miliyan guda a karon farko, wato a jimlace ya kai mutane 1,001,581.

A watan Yuni, Africa CDC ta kaddamar da wani gagarumin shirin hadin gwiwa don kara yawan gwaje gwajen cutar COVID-19 a Afrika, wato PACT a takaice, wanda ya kunshe muhimman jigogi uku: gwaji, bin diddigi, da kuma warkar da masu dauke da cutar.

A cewar Nkengasong jami'in Afrika CDC, an kaddamar da shirin gwaje gwajen cutar ta COVID-19 ne ga mutanen nahiyar, da bin diddigin mutanen da suka yi mu'amala da masu dauke da cutar, da kuma kula da lafiyar mutanen da suka harbu da cutar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China