2020-08-31 09:44:27 cri |
Sai dai shugaban kasar ya ce kafofin shiga kasar na kasa da ruwa, za su ci gaba da kasancewa a rufe.
Nana Akufo Addo ya bayyana cikin jawabin da ya yi wa kasar cewa, ana bukatar kowanne matafiyi da zai shiga kasar, ya gabatar da sakamakon gwajin da ya yi a wani amintaccen dakin gwaji na kasarsa, dake nuna ba shi da cutar COVID-19.
Ya kara da cewa, za a yi wa kowanne fasinja da zai sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Kotoka, gwajin cutar kan wani farashi da matafiyin zai biya, yana mai cewa za a samu sakamako cikin mintuna 30.
Har ila yau, ya ce gwamnati zata tabbatar da cewa, sassauta matakai a hankali, ciki har da bude filayen jiragen sama, ba su kai ga sake bullar cutar a kasar ba. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China