![]() |
|
2020-09-02 10:47:21 cri |
A cewar sharhin, kasar Sin ta kwace kashi mafi yawa na kasuwannin duniya a wannan kakar daga kamfanoni sauran kasashen duniya, inda zata cigaba da mamaye kasuwannin duniya na dogon lokaci kafin duniya ta farfado daga annobar.
Sharhin ya nuna cewa, kasar Sin ta yi amfani da takaitattun kudade, kwararrun 'yan kwadago da ingantattun kayayyakin more rayuwa, kana ta kuma yi amfani da bankuna mallakar gwamnatin kasar wajen bayar da rancen kudaden tallafawa kananan da manyan 'yan kasuwa domin jurewa tasirin annobar, kasar Sin tana samun karfin fitar da kayayyaki zuwa ketare, wacce bata samu wata illa daga annobar COVID-19 da kuma harajin kwastan na Amurka ba.
Rajiv Biswas, wani kwararren masanin tattalin arzikin Asiya na kamfanin IHS Markit, wani babban kamfanin kwararru da kuma tattara alkaluma na duniya, ya bayyana cewa, adadin cinikayyar kasar Sin zuwa ketare ya karu da kusan kashi 20 bisa 100 a rubu'i na biyu na wannan shekarar, inda ya karu da kashi 12.8 bisa 100 a shekarar 2018 da kashi 13.1 bisa 100 a shekarar bara, a cewar sharhin. A yanzu ta bayyana a fili kasar Sin ta samu babban karfi ta fuskar fitar da kayayyakinta zuwa kasashen waje daga fannoni masu yawa. Hada hadar cinikayyar kasar Sin yayi matukar karuwa a lokacin kakar wannan shekarara, musamman a watan Yuli. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China