![]() |
|
2020-09-01 09:29:29 cri |
Kudurin hukuntawa, da gyara halayyar 'yan ta'addan kasashen ketare, da aka kadawa kuri'u a yayin taron kwamitin tsaron MDD na jiya Litinin, ya gaza samun cikakken goyon baya, bayan da Amurka ta ki kada masa kuri'ar amincewa.
Baya ga kasar Amurka, sauran mambobin kwamitin 14 sun amince da wannan kuduri, wanda ke jaddada kiran da aka jima ana yi, game da ci gaba da aiwatar da matakan hukunta 'yan ta'addan kasashen ketare tsakanin kasa da kasa, da aiwatar da matakan gyara halayen su idan bukatar hakan ta taso, tare da sake shigar da su cikin al'umma, kamar dai yadda kudurorin da suka gabaci hakan suka tanada.
Kwamitin tsaron MDD yana zartas da kudurorin sa ne karkashin tsarin gabatar da takardun amincewa, ta hanyar kada kuri'u cikin yanayi na musamman, sakamakon kokarin da ake yi na dakile cutar COVID-19, bisa tanadin wasikar kasar Sin, mai jagorancin zaman kwamitin na watan Maris. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China