Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sudan: Yarjejeniya da kungiyoyi masu dauke da makamai mataki ne na farko na samar da cikakken zaman lafiya
2020-08-31 09:52:11        cri
Firaministan Sudan Abdalla Hamdok, ya ce yarjejeniyar zaman lafiya da aka shirya rattabawa hannu a yau Litinin, tsakanin gwamnatin kasar da kungiyoyi masu dauke da makamai, mataki ne na farko na samar da cikakken zaman lafiya.

Abdallah Hamdok ya bayyana a jiya cewa, yarjejeniyar zata ba su sabon kuzarin ci gaba da bin tafarkin aiwatar da karin ayyuka, ciki har da inganta zaman lafiya a aikace a cikin al'ummomin da kammala matakan samar da cikakken zaman lafiya a matsayin hanyar cika burin al'ummar kasar na samun adalci da zaman lafiya da ci gaba.

Ya ce wannan lokaci ne na yin kyakkyawan fata game da abun da suka cimma tare da 'yan kasar.

Da farko a jiyan, Abdalla Hamdok ya tafi Juba, babban birnin Sudan ta Kudu, domin halartar bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ta zaman lafiya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China