Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ghana za ta sake bude kan iyakokinta yayin da masu kamuwa da COVID-19 ke raguwa
2020-08-17 21:25:00        cri
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya bayyana cewa, kasarsa na duba yiwuwar sake bude kan iyakokinta a ranar 1 ga watan Satumban dake tafe, yayin da ake samun raguwar sabbin masu kamuwa da cutar COVID-19 .

Shugaban wanda ya bayyana haka ne, a jawabinsa karo na 15 ga 'yan kasar kan cutar COVID-19 a daren ranar Lahadi, ya ce shawarar sake bude kan iyakokin kasar, ta dogara ne kan aikin shirye-shiryen da hukumomi masu ruwa da tsaki suka gudanar.

Sai dai kuma, ya bayyana cewa, za a ci gaba da ba da kulawa ta musamman wajen kwashe 'yan kasar ta Ghana da suka makale a kasashen waje, za kuma a bukace su da su bi matakan killacewa na tilsa da ka'idojin kariya na musamman da aka tanada.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China