Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Gurgunta kamfanonin ketare da wasu 'yan siyasar Amurka ke yi ya haifar da hasara ga kamfanonin kasashe daban daban
2020-08-27 20:12:41        cri

A yau yayin taron ganawa da manema labaran da aka yi a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana cewa, wasu 'yan siyasar Amurka, na gurgunta kamfanonin da ba na kasar Amurka ba, bisa fakewa da batun tsaron kasa, lamarin ya riga ya harfar da hasara ga masu sayayya, da kamfanonin na kasa da kasa, ciki har da na Amurka ita kanta, kuma tabbas hakan zai gamu da adawa daga kasashen duniya.

Rahotanni sun nuna cewa, a jiya Laraba kungiyar 'yan kasuwar Amurka, ta fitar da wani sakamakon bincike, game da kamfanonin Amurka dake kasar Sin, inda aka bayyana cewa, kaso 90 bisa dari na kamfanonin da aka yi musu bincike na ganin cewa, matakin da gwamnatin Amurka ta dauka kan manhajar WeChat, zai yi mummunan tasiri ga harkokin kamfanoninsu.

Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, matakin da Amurka ta dauka, ya sabawa ka'idar adalci da Amurka take cewa tana bi a ko da yaushe, kuma ya keta ka'idar kasa da kasa, kana ya lalata yanayin cudanya, da hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, a bangaren kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China