Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi tir da kalaman raba kawuna na shugaba Trump
2020-08-24 20:34:43        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya ce maimakon daukar matakan raba kawuna, kamata ya yi shugabannin Amurka su aiwatar da dabarun dinke baraka, da inganta hadin gwiwa da Sin.

Zhao Lijian ya bayyana hakan ne yau Litinin, yayin taron manema labarai na rana rana a nan birnin Beijing. Jami'in ya soki kalaman shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya ayyana cewa, akwai yiwuwar raba gari tsakanin tattalin arzikin kasar sa da na Sin. Yayin wata ganawa da kafar watsa labarai ta Fox News a jiya Lahadi, Mr. Trump ya bayyana cewa, ba lallai ne sai Amurka ta yi cudanyar kasuwanci da kasar Sin ba.

Game da hakan, Mr. Zhao ya ce hadin gwiwar Sin da Amurka, ya amfani sassan biyu tsawon shekaru sama da 40 da kafuwar huldar diflomasiyyar su, kuma ci gaban kasashen biyu ba wai yana amfanar bangare daya ba ne, duba da cewa dukkanin sassan suna amfana, kuma kamata ya yi a kara fadada cudanya, maimakon furka aniyar raba-gari.

Zhao ya ce kamata ya yi Sin da Amurka, su yi aiki kafada da kafada da juna, wajen sauke nauyin duniya dake wuyan su, yana mai cewa, duniya ta riga ta dunkule waje guda, kuma ba wata kasa guda daya tilo, da za ta iya shawo kan tulin kalubalen ta ita kadai, musamman ma batun yaki da cutar numfashi ta COVID-19, da kuma yunkurin farfado da tattalin arziki.

A cewar sa, yunkurin warware matsala ta hanyar rabuwa ba zai haifar da 'da mai ido ba, maimakon hakan, matakin zai cutar da kasar da ta yi yunkurin yin hakan ne, da ma al'ummun ta baki daya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China