2020-08-27 20:07:12 cri |
Rahotanni sun nuna cewa, ana gudanar da zanga-zanga a sassa daban daban na kasar Amurka, sakamakon harben wani saurayi bakar fata mai suna Jacob Blake a birnin Kenosha na jihar Wisconsin da wani dan sanda ya yi.
Game da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi yau cewa, a cikin 'yan kwanakin suka gabata, irin wannan lamari ya faru sau da dama, wanda hakan ke matukar jawo hankalin al'ummun kasashen duniya.
Jami'in ya kara da cewa, ya kamata gwamnatin Amurka ta saurari bukatun tsirarun al'ummun kasar, don tabbatar da daidaito da adalci, kuma ya dace ta mai da hankali kan damuwar da kasashen duniya suke nunawa ga yanayin hakkin dan Adam da kasar ke ciki. Haka kuma, ta daidaita matsalar nuna wariyar launin fata mai tsanani da ake fuskanta a kasar.
A watan Yunin bana, hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD ta zartas da wani kuduri, inda ta yi suka da kakkausar murya, game da kisan saurayi bakar fata George Floyd, a ranar 25 ga watan Mayun bana, ta kuma yi kira ga Amurka da ta dauki hakikanin matakai, na kiyaye hakkin dan Adam, da zaman walwala mai tushe na Amurkawa 'yan asalin nahiyar Afirka. (Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China