2020-08-24 20:01:55 cri |
Gwamnatin kasar Sin ta ce tana goyon bayan kamfanonin kasar bisa aniyar su ta kare hakkin su gaban kuliya daga muzgunawar da gwamnatin Amurka ke musu. Hakan dai na zuwa ne bayan da kamfanin yada bidiyo na TikTok ya sanar da aniyar shigar da gwamnatin shugaba Trump na Amurka gaban kuliya.
Kakakin ma'aikatar wajen Sin Zhao Lijian, ya shaidawa taron manema labarai na rana rana cewa, Sin za ta ci gaba da aiwatar da matakai na kare halastaccen hakki da moriyar kamfaninin kasar.
Ya ce "mutanen nan sun cutar da kamfanin TikTok, da ma wasu karin kamfanonin Sin ta hanyar fakewa da tsaron kasa, kuma bayanan su cike suke da karairayi da bata suna, duka da nufin nuna fin karfi da almundahana.
Mr. Zhao ya kara da cewa, ayyukan wasu daga 'yan siyasar Amurka cike suke da dabarun gurgunta tattalin arzikin kamfanonin da ba na Amurka ba ne, musamman masu fifiko a wasu fannoni.
Daga nan sai ya bayyana matakin na Amurka a matsayin yunkurin dakushe kasuwannin wasu kamfanoni, da karya tsarin daidaito a fannin takara, wanda hakan ya sabawa ka'idojin cinikayya na kasa da kasa, wanda ke illa ga sha'anin musaya da hadin gwiwar kimiyyar kirkire kirkire mai dacewa da yanayin wayewar duniya. Zhao ya ce a yanzu duniya na kara fahimtar halayyar Amurka ta sata da kwace. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China