Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kamfanin Fujifilm: Ficewa daga kasuwannin Sin rashin tunani ne
2020-08-19 16:46:53        cri

Annobar shakewar numfashi ta COVID-19 ta haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya. Tattalin arzikin kasar Sin ya jure tasirin annobar, hakan ya nuna cewa, akwai yiwuwar samun kyakkyawar makoma ga tattalin arzikin kasar a nan gaba. A hannu guda kuma, kasar Sin tana ci gaba da bude kofarta ga kasashen duniya kuma tana ci gaba da taka rawa wajen bunkasa tattalin arziki tare da yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya. A watanni shidan farko na wannan shekara, kamfanonin kasashen waje masu yawa suna ci gaba da fadada hannayen jarinsu a kasar Sin kuma suna samun gagarumin ci gaba.

A yayin tattaunawa da kafar yada labarai ta gidan talabijin na CCTV, shugaban kamfanin zuba jari na Fujifilm na kasar Sin, Taketomi Hironobu ya ce, tsarin kasuwancin zai ci gaba da aiwatar da sauye sauyen da aka samu a kasuwannin kasar Sin wanda ya kuma dace da manufofin ci gaban kasar Sin. Ya kuma kara da cewa, kamfanin zai ci gaba da neman hanyoyin da za su kara rubanya cinikin da yake samu a duk shekara.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China