Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Japan ta yi bikin cika shekaru 75 da mika wuyan da dakarunta suka yi lamarin da ya kawo karshen yakin duniya na biyu
2020-08-15 21:23:25        cri
A ranar Asabar kasar Japan ta yi bikin tunawa da cika shekaru 75 da mika wuyan da dakarunta suka yi lamarin da ya kawo karshen yakin duniya na biyu, inda basaraken kasar Naruhito ya bayyana juyayi game da halin da Japan din ta tsinci kanta a lokacin yakin, an gudanar da bikin ne da sanyin safiya a birnin Tokyo.

Basaraken da uwargidansa, gami da firaministan kasar Shinzo Abe da wasu mutane 'yan tsiraru ne suka halarci bikin sakamakon matakan da ake dauka domin takaita yaduwar annobar COVID-19.

Abe, wanda ya zaku game da yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska tun bayan kawo karshen yakin, bai yi wani tsokaci game da yanayin tashin hankalin da Japan din ta shiga ba a lokacin yakin duniyar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China