Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mai yiwuwa Sin za ta mayar da martani ga matakin da Amurka ta dauka kan kwalejin Confucius
2020-08-14 21:05:40        cri

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, ya ba da sanarwa kwanan baya, inda ya nemi kwalejin Confucuis reshen Amurka, ta yi rajista a matsayin "Tawagar diflomasiyya".

Game da wannan batu, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya shaidawa manema labarai a yau Juma'a cewa, wannan mataki tamkar shafawa aikin hadin kan kasashen biyu bakin fenti ne, kuma Sin na matukar nuna rashin jin dadinta game da hakan, kuma mai yiwuwa ta mayar da martani.

A cewar Zhao, kwalejin ta kasance kamar wata gada ce dake taimakawa al'umomin kasashen duniya koyon harshen Sinanci da fahimtar al'adun Sinawa, da kara yin mu'ammala da hadin kai ta fuskar ba da ilmi da raya al'adu, wadanda ake tafiyar da su a fili bisa adalci, kuma bisa doka.

Kaza lika hakan nacewa ne ga ka'idojin jami'o'i daban-daban, kuma kwalejin ta ba da babbar gudunmawa wajen kara kyautata mu'ammala tsakanin jama'ar kasashen Sin da Amurka, dalilin da ya sa take kara samun karbuwa matuka daga jami'o'i, da bangarori daban-daban a Amurka. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China