Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta cafke 'yan kasashen waje 3 bisa laifin fasakwaurin makamai
2020-08-19 10:42:08        cri

Sojojin Najeriya sun kama baki 'yan kasashen waje uku da suke da hannu a safarar makamai zuwa kasar, kamar yadda jami'ai suka tabbatar a ranar Litinin.

Da yake jawabi ga 'yan jaridu a jihar Katsina dake arewacin kasar, kakakin rundunar sojojin Najeriya, Benard Onyeuko, ya ce ana tuhumar bakin uku 'yan kasar Nijer da laifin samarwa bata gari makamai domin aikata ta'addanci a shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Ya ce an cafke mutanen uku ne a gundumar Dantudu-Malailai dake Sabon-Birni a jihar Sokoto a ranar Asabar.

Hare haren da barayi ke kaddamarwa na baya bayan nan sun jefa rayuwar mazauna shiyyar arewa maso yammacin Najeriya cikin tashin hankali, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe rayukan fararen hula, da satar shanu, da yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Sojojin Najeriya suna cigaba da kaddamar da aikin sintiri a shiyyar domin murkushe kungiyoyin 'yan bindiga dake addabar yankin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China