Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya: kasar Sin ta kasance wata dama mai kyau ga bunkasuwar kasashen Afrika
2020-08-15 21:36:28        cri

Cibiyar nazarin kasar Sin ta Najeriya ta wallafa wata sanarwa mai taken "Sin ba ta keta ko wani ikon mulki kan sauran kasashe ba" a jaridun "Leadership" da "Poeples Daily" da dai sauransu a kwanan baya. A ganin wannan sanarwa, Sin ta nace ga samun bunkasuwa cikin lumana da mutunta muradun sauran kasashe, rancen kudin da Sin ta baiwa Afrika da nufin taimaka masu wajen fita daga kangin talauci, matakin da ba zai illata kasashen Afrika ba, kuma suna cin gajiyarsa matuka.

Ban da wannan kuma, sanarwar ta ce, ra'ayin da aka bayar kwanan baya wai bada tallafi ta hanyar rancen kudin da Sin take baiwa Najeriya ya keta ikon mulkin Najeriya, babu wani gaskiya a ciki. Sin tana taimakawa kasashen Afrika wajen gaggauta zamanantar da al'umma da bunkasuwar tattalin arziki ta hanyar bada tallafin rancen kudi. Bugu da kari, bunkasuwar kasar Sin na da alaka matuka da rancen kudin da ta samu daga kasashen duniya. Rancen kudin da Sin ta samarwa Najeriya da zummar kara hadin kan kasashen biyu don bada tabbaci ga bunkasuwar Najeriya.

Sannan, sanarwar ta ce, Sin ta kan aiwatar ka'idoji biyar na yin zama tare cikin lumana. A shekarar 2006, ta nanata wannan matsayi yayin da ta gabatar da manufofi dangane da Afrika tare kuma da jaddada wajibcin mutunta hanyar da kasashen Afrika suke bi da kuma mutunta kokarin da kasashen Afrika suke yi don ingiza bunkasuwar tattalin arziki da al'ummarsu da ma kyautata zaman rayuwar jama'arsu. Nazarin da aka gudanar ya nuna cewa, Sin muhimmiyar abokiya ce ga kasashen Afrika, ita kuma wata dama ce mai kyau gare su wajen samun bunkasuwa da kuma cike gibin da suke da su a fannin kudade, da kimiyya da karfi da dai sauransu, Sin tana da karfi kuma tana fatan taimakawa kasashen Afrika don tinkarar manyan kalubaloli. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China