Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan Sin sun jaddada bukatar ilimantar da matasa batun kare hakkin bil-Adama
2020-08-14 13:04:20        cri

Masana da dama na kasar Sin sun jaddada bukatar a rika ilimantar da matasa game da abubuwan da suka shafi kare hakkin bil-Adama, a wani mataki na ciyar da batun kare hakkin bil-Adama gaba yadda ya kamata.

Mamba a cibiyar nazarin kare hakkin bil-Adama ta kasar Sin (CSHRS) Qian Jinyu, shi ne ya bayyana haka, yayin wani taron dandalin kare hakkin dan-Adam na kasa da kasa da cibiyar kare hakkin dan-Adam dake kasar Uzbekistan ta shirya ta kafar bidiyo. Yana mai cewa, yadda matakin zai ci gajiyar ci gaba mai dorewa, ya dogara kan ko matasan za su shiga a dama da su, ta hanyar irin wannan ilimantarwar.

Qian ya ce, sai matasa daga kasashen daban-daban sun rungumi batun ci gaba da zai shafi kowa, sannan aka dama da su wajen gina duniya mai cike da zaman lafiya da kare hakkin dan-Adam, da yadda ake tafiyar da batun kare hakkin bil-Adama a duniya ne kadai za su bayar amsoshi masu gamsarwa game da makomar bil-Adama.

A nasa jawabin, He Zhipeng, zaunannen mamba a hukumar CSHRS, ya bayyana cewa, ilimantar da matasa game da batun kare hakkin dan-Adam, ita ce muhimmiyar hanyar da matasan za su gyara tunaninsu da kuma batun shugabanci na gari. Kuma hanya daya ta auna matakin da kasa ke dauka game da kare hakki bil-Adama da nasarorin da ta samu, ita ce bayan ta yi na'am da mabambantan damuwar da kasashe ke da su game da batun da ya shafi kare hakkin dan-Adam. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China