Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya na fatan zama babbar cibiyar samar da zinari a yammacin Afirka
2020-08-11 19:49:09        cri
Ministan ma'aikatar hakar ma'adanai da bunkasa sarrafa karafa a Najeriya Olamilekan Adegbite, ya ce kasar na fatan zama babbar cibiyar samar da ma'adanin zinari a yammacin Afirka, duba da irin tarin zinari da kasar ke da shi a karkashin kasa, da kuma yawan al'umma dake iya shiga ayyukan kwadago.

Mr. Adegbite wanda ke wannan tsokaci, yayin ganawa da 'yan jarida a jiya Litinin, ya ce wannan manufa za ta samar da zarafin fadada kudaden shigar da kasar ke samu, baya ga fannin albarkatun danyen mai, kana hakan zai samar da dunbin guraben ayyukan yi ga matasan kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China