Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta tanadi da karin kudi don samar da kayan jin kai na bukatun gaggawa
2020-08-06 09:52:07        cri
Ma'aikatar kudi ta kasar Sin, ta ware kudin kasar har yuan biliyan 30, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 4.3, don samar da kayayyakin da ake bukata, a lokutan gudanar da ayyukan jin kai na gaggawa.

Ma'aikatar wadda ta bayyana hakan a kan shafin ta na yanar gizo, ta ce za a yi amfani da kudaden wajen samar da kayayyakin bukata, kari kan wadanda kananan yankuna ke tanada, a wani mataki na kafa tsari mai inganci na tabbatar da jagoranci, da tara kayayyakin bukata, da raba su a duk lokacin da bukatar gaggawa ta bijiro.

Kaza lika ma'aikatar kudin ta ce, gwamnatin Sin za ta maida hankali ga batun magance matsalolin kamfar kayayyakin bukatar gaggawa a matakin farko na al'umma, kana za ta tabbatar da an tanaji isassun kayan bukata yadda ya kamata, da sauran kayan kiwon lafiya, da suka hada da magunguna, da kayan kariyar lafiya da na bada jinya.

Daga nan sai ma'aikatar ta yi kira ga gwamnatocin lardunan kasar, da su kara inganta matakan yin tanadin muhimman kayayyakin da ake bukata a lokuta na gaggawa, su kuma karfafa gwiwar kamfanoni wajen tanadar tsarin sarrafa irin wadannan kayayyaki na kula da lafiya, da samar da karin su cikin sauri idan da bukata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China