2020-08-07 10:08:34 cri |
Bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayoyi game da huldar dake tsakanin kasashen biyu, da dangantakar soji a tsakaninsu, kana da batun huldar musayar sojoji tsakanin kasashen biyu a zagaye na gaba.
Wei, ya bayyana matsayar kasar Sin game da wasu batutuwa da suka hada da batun tekun dake kudancin kasar Sin, da batun yankin Taiwan, da nuna kyamar da Amurka ke yiwa kasar Sin, inda ya bukaci bangaren Amurka da ta dena furta kalaman batanci ko kuma aikata mummunan aiki kan kasar Sin, a yi kokarin ingantawa da kuma tabbatar da harkokin tsaro dake shafar tekuna, kana a guji yin duk wani mummunan yunkuri wanda zai iya lalata yanayin da ake ciki, kuma a yi kokarin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin shiyyoyin.
Esper a nasa bangaren yace, yayin da ake fuskantar zaman tankiya tsakanin kasashen biyu, ya kamata bangaren sojojin kasashen biyu su mayar da hankali kan tattaunawa da tuntubar juna domin warware duk wani sabani, kuma su guji yiwa juna mummunar fassara da kuma rage abubuwan da zasu haifar da barazana a tsakaninsu. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China