Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masani: Amurka zata tafka hasara yayin da shugaba Trump ke neman matsawa TikTok lamba
2020-08-09 16:49:36        cri
Wani masanin kasar Amurka ya yi gargadin cewa, yayin da gwamnatin Trump ke neman hana yin amfani da wasu APP wato manhajoji masu farin jini irinsu TikTok da WeChat, kasar Amurka zata iya tafka babbar hasara sakamakon wannan matakin da ake dauka.

Wei Shangjin, wani shehun malami mai nazarin hada-hadar kudi da tattalin arziki dake aiki a jami'ar Columbia ta kasar Amurka, ya ce yadda ake neman tilasta a sayar da kamfanin TikTok da wani farashi mai rahusa ga wani kamfanin kasar Amurka zai iya haifar da hadari ga kamfanonin kasar Amurka da yawa, wadanda ke zuba jari a kasar Sin.

A ranar Alhamis da ta gabata, shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya bada umarni, inda ya hana kamfanonin kasar Amurka mu'amala da kamfanin ByteDance na kasar Sin, wanda ke mallakar TikTok a halin yanzu, cikin kwanaki 45.

Cikin wannan umarnin da shugaban Trump ya bayar, ya ce an taba sauke APP din TikTok har fiye da karo miliyan 175 a kasar Amurka, gami da fiye da karo biliyan 1 a duk duniya. Yana zargin APP din da satan bayanan masu yin amfani da shi, lamarin da a cewarsa zai haifar da barazana ga tsaron kasar Amurka. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China