Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya ta kaddamar da shirin MDD na samar wa matasa damammaki
2020-08-06 10:15:53        cri
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya kaddamar da wani shiri mai taken GenU, wani shiri ne na MDD wanda zai taimakawa gwamnatin Kenya wajen samar da damammaki ga matasan kasar.

Kenyatta ya ce, matasa su ne kusan kashi daya bisa uku na yawan jama'ar kasar Kenya. Ya kara da cewa, gwamnatin kasar ta kara zuba jari a fannonin inganta rayuwar matasa kamar bangaren ilmi, fasahar zamani, da kuma fannin samar da sana'o'in dogaro da kai a shekaru masu yawa da suka gabata sakamakon hasashen irin dimbin gudummawar da matasan za su bayar wajen bunkasuwar tattalin arzikin kasar.

A sanarwar da aka fitar bayan kammala taron kaddamar da shirin wanda aka gudanar ta kafar bidiyo a Nairobi, shugaban ya ce, sakamakon muhimmanci shirin na GenU ya sa shugaban kasar ya amince da shi a matsayin wani muhimmin dandali, wanda zai baiwa shugabanni, da abokan hulda, da masu ruwa da tsaki damar zuba jari wanda zai iya samar da damammaki ga matasan kasar ta Kenya.

Shi dai wannan shiri na GenU, shiri ne na bunkasa ci gaban matasa na MDD wanda aka kaddamar a shekarar 2018 da zummar tallafawa rayuwar matasa daga 'yan shekaru 10 zuwa 24 domin ba su damar shiga makarantu don samun ilmi, ko samun horo, ko kuma samar musu guraben ayyukan yi nan da shekarar 2030. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China