Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya za ta yi rangwamen haraji a fannin kudaden dakon kaya ta layin dogo na Mombasa-Naivasha
2020-06-29 14:10:54        cri
Kenya ta alkawarta samar da rangwamen haraji, a fannin kudaden dakon kayayyaki ga masu sufurin hajoji tsakanin layin dogo na Mombasa zuwa Naivasha. Hukumar layin dogo ta Kenya ta ce wannan garabasa za ta kare ne a ranar 30 ga watan Agustan dake tafe.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce a baya, harajin sufurin kwantaina mai tsawon kafa 20 daga Mombasa zuwa Naivasha ya kai shillings 51,144, kwanankwacin dalar Amurka 480, a yayin da harajin ya kai dalar Amurka 240 daga Naivasha zuwa Mombasa. Kaza lika bisa farashin na yanzu, kwantaina maras kaya za a dauke ta a kan dala 120.

Kenya ta kaddamar da zirga zirga kan layin dogo na SGR tsakanin Mombasa zuwa Nairobi tun a watan Disambar 2017, kafin daga bisani aka kaddamar da hidimar dakon kaya tsakanin Nairobi zuwa Naivasha daga watan Disambar shekarar 2019. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China