Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutanen da suka kamu da COVID-19 ya kai 859237 a Afrika
2020-07-29 09:30:33        cri

Cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta ce adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a duk fadin Afrika ya kai 859,237 ya zuwa ranar Talata.

Africa CDC, kwararriyar hukumar lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika AU, mai mambobin kasashe 55, a sabbin bayanan da ta bayar a ranar Talata ta ce, adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar COVID-19 a fadin nahiyar ya karu daga 846,311 a ranar Litinin zuwa 859,237 da tsakiyar ranar Talata, wato an samu sabbin kamu kusan 13,000 a cikin wannan wa'adi da aka ambata.

Africa CDC ta kuma ba da rahoto cewa, adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar annobar ta COVID-19 ya karu zuwa 18,160 a ranar Talata, daga adadin mutane 17,747 a ranar Litinin.

Sai dai cibiyar ta tabbatar cewa, marasa lafiyar da suka warke daga cutar COVID-19 ya kai 506,534 ya zuwa yanzu a duk fadin nahiyar.

Afrika ta kudu, a halin yanzu ta ba da rahoton mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a kasar kimanin 452,529, ita ce kasa mafi yawan masu fama da cutar a Afrika, sai kasashen Masar, Najeriya, Algeria da Morocco dake bi mata baya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China