Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin sulhu ya tsawaita takunkumi da aka sanyawa masu kawo barna ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka ta Tsakiya
2020-07-30 14:36:43        cri

A ranar 28 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2536, inda za a tsawaita takunkumin da aka sanyawa masu kawo barna ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Afirka ta Tsakiya na tsawon shekara guda, wato zuwa ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2021, wadanda suka hada da haramcin sayan makamai da hana tafiye-tafiye da ma haramta amfani da kadarorinsu da dai sauransu. Sa'an nan za a tsawaita wa'adin aikin kungiyar kwararru masu kula da takunkumin har zuwa ranar 31 ga watan Agustan shekarar badi. (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China