Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rikici yayi sanadiyyar rayukan mutane 40 a jamhuriyar tsakiyar Afrika
2019-12-27 09:41:10        cri
A kalla mutane 40 aka kashe a yayin wani rikici da ya barke tsakanin 'yan kasuwa, da kungiyoyin 'yan tada kayar baya a Bangui, babban birnin jamhuriyar tsakiyar Afrika, tun daga lokacin fara bukukuwan kirsimeti, wata majiya daga yankin ta tabbatar da faruwar lamarin.

Rikicin ya barke ne a babbar kasuwar PK5, dake tsakiyar Bangui, kuma ta k\asance babbar mafakar mayakan 'yan tawayen. A cewar wasu mazauna yankin da suka bukaci a sakaye sunansu, kungiyoyin 'yan tada kayar bayan sun nemi 'yan kasuwa dake da shaguna a kasuwar da su biya su kudaden haraji na cinikin da suka yi na kayayyakin kyaututtukan bikin kirsimeti, lamarin da ya haddasa takaddama har tayi sanadiyyar kashe guda daga cikin 'yan tada kayar bayan. Daga bisani rikicin ya rikide zuwa kazamin fada tsakanin bangarorin biyu.

An yi ta jiyo karar harbe harben bindiga daga babbar kasuwar ta PK5 a lokacin da ake gwabza fadan, wanda ya yi Kamari da safiyar ranar Alhamis inda 'yan tawayen suka cinna wuta a wasu shagunan 'yan kasuwar. Daga bisani hankulla sun kwanta bayan gudanar da aikin wanzar da tsaro na hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaron kasar da dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD.

Ba'a samu mutuwar jami'in tsaro a wajen ba. Wasu shaidun gani da ido sun ce an kashe mutane 40 daga dukkan bangarorin biyu.

Sai dai harkokin kasuwanci sun durkushe a kasuwar ta PK5 a ranar Alhamis, kana an samu matsalar cunkoson ababen hawa, yayin da ake cigaba da samun wasu dake kona tayoyi akan titinan dake kusa da wajen. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China