2020-07-30 10:46:33 cri |
Monica Gandhi, wata kwararriya a fannin cutuka masu yaduwa a jami'ar California, San Francisco, ta yi sharhi cewa: "A wasu kasashen duniya, mutane sun fara amfani da takunkumin rufe baki da hanci da zarar aka samu barkewar annobar, kuma yawan mutanen da suka mutu a kasar ba su da yawa." Rashin samar da isassun takunkuman rufe baki da hanci ga al'umma a kan lokaci, mai yiwuwa shi ne babban kuskuren da Amurka ta tafka" daga cikin jerin matakan yaki da annobar, in ji Monica.
Jaridar "The Washington Post" ta bayyana cewa, yanayin da aka fada ciki ya faru ne sakamakon rudani da aka samu game da dokokin gwamnati, batun halayyar Amurkawa na bijirewa amfani da takunkumin rufe baki da hanci da siyasantar da batun annobar. Shugaban Amurka Donald Trump ya ki yarda ya sanya takunkumin sannan ya nunawa sauran jama'a kada su sanya takunkumin, hakan na daga cikin dalilan da suka taka rawa ga tabarbarewar al'amurran cutar a kasar. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China