Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
The Lancet: har yanzu kasashen duniya na iya koyi da kasar Sin wajen yaki da COVID-19
2020-07-25 20:32:54        cri

Mujallar The Lancet mai wallafa batutuwan da suka shafi kiwon lafiya, ta ce kasar Sin ta yi nasarar dakile yaduwar COVID-19, kuma sauran sassan duniya na iya koyi daga nasarorinta wajen dakile cutar.

Mujallar ta bayyana cikin wata mukalar da ta wallafa a baya-bayan nan cewa, yadda kasar Sin ta tunkari cutar ya nuna muhimmancin aiwatar da bincike a cikin gida da kuma karfin tsarin kiwon lafiyar al'umma.

Ta ce masana kimiyya na kasar Sin sun yi gaggawar gano kwayar cutar tare da sanar da bayananta ga kasa da kasa jim kadan bayan bullarta, haka zalika kasar Sin na kan gaba wajen binciken riga kafi.

Baya ga haka, ta ce nasarar gaggauta aiwatar da matakan dakile COVID-19 na matukar bukatar damawa da al'umma, kuma an ga yadda hadin kan al'umma yake fiye da a yaushe, yayin barkewar cutar a kasar Sin.

Bugu da kari, mukalar ta ce dakile wata annobar lafiya da ta shafi duniya na bukatar hadin gwiwa bisa gaskiya, kuma idan ana batun COVID-19, dorawa kasar Sin laifi ba abu ne da ya dace ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China