Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mujallar Nature Microbiology: Kila Nauin Cutar COVID-19 Ta Yaduwa Tsakanin Jamega Na Goman Shekaru
2020-07-30 10:31:30        cri

Kwanan baya, mujallar kimiyya ta Nature Microbiology ta wallafa wani sakamakon nazarin wata tawagar kasa da kasa ta yi a kan Intanet cewa, nau'in cutar SARS-CoV-2 wadda ta haddasa COVID-19 ta sauya ne daga wata cuta dake da alaka matuka da ita daga shekaru 40 zuwa 70 da suka gabata, a hakika, irin wannan cuta tana yaduwa tsakanin jamega na goman shekaru. Masu binciken sun yi imanin cewa, gano asalin cutar yana da muhimmanci sosai wajen kandagarkin cutar. Tawagar masanan sun fito ne daga jami'ar jihar Pennsylvania ta Amurka da jami'ar Edinburgh ta Birtaniya da jami'ar Hongkong ta kasar Sin da dai sauransu.

Kafar watsa labarai ta kasar Birtaniya BBC ta ba da labari cewa, wannan sakamako ya karyata makarkashiya da aka yi wai an harhada wannan cuta ce a dakin gwaji ko Bil Adama ne suka kirkiro wannan cuta da dai sauransu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China