Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda suka kamu da COVID-19 a Afrika ya kai 846311
2020-07-28 09:18:07        cri

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta nahiyar Afrika (Africa CDC), ta ce adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a fadin nahiyar, ya kai 846,311 a jiya Litinin.

Cibiyar Africa CDC ta kara da cewa, yawan wadanda cutar ta yi ajalinsu, ya karu zuwa 17,747, zuwa safiyar jiyan.

Cibiyar ta kuma jaddada cewa, wasu mutane 491,889 da suka kamu da cutar sun riga sun warke.

Cutar ta fi kamari a kasar Afrika ta kudu, wadda ta ba da rahoton tabbatar da mutane 445,433 sun kamu, sai kuma kasashen Masar da Nijeriya da Algeria da Morocco. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China