Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta gina tashoshin fasahar 5G kimanin 410,000 zuwa watan Yuni
2020-07-27 10:09:39        cri

Kasar Sin ta gina sabbin tashoshin fasahar zamani ta 5G guda 257,000 a watanni shidan farkon wannan shekara, ma'aikatar kula da masana'antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, MIIT ta tabbatar da hakan.

Baki dayan adadin tashoshin ya kai 410,000 ya zuwa karshen watan Yuni, kamar yadda alkaluman da MIIT ta fitar ya nuna.

Wen Ku, wani jami'i dake aiki da ma'aikatar MIIT ya ce, adadin wayoyin hannu masu fasahar 5G da aka samar a kasar Sin ya kai miliyan 86.23, yayin da yawan mutanen dake amfani da fasahar ta 5G ya kai miliyan 66 ya zuwa karshen watan Yuni.

Adadin darajar fasahar ta 5G da aka samar wajen yada bayanai, da amfani da manhajoji, da ayyukan hidimar fasahar sadarwa ta zamani ya karu zuwa kashi 14.5 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara, kana ya karu da kashi 1.3 bisa 100, bisa watannin uku na farkon shekarar bana.

Wen ya kara da cewa, akwai bukatar aiwatar da karin manufofi domin bunkasa darajar kasuwar fasahar, ya kamata a kara karfafa hadin gwiwar kasa da kasa game da fasahar ta 5G, tare da kuma kyautata dabarun amfani da fasahar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China