![]() |
|
2020-07-22 21:10:20 cri |
Kwanan baya, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya fake da annobar cutar numfashi ta COVID-19, inda ya bata sunan kasar Sin ta kowace fuska. Ya kuma zargi dama takalar kasar Sin ta fuskar tunani, tare da rura wutar cewa, kasar Sin na kawo barazana. Dangane da lamarin, Wang Wenbin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Laraba a nan Beijing cewa, wasu maganganun da Mike Pompeo ke yi cike suke da karairayi da rudarwa, wadanda suka nuna kuskuren da Amurka ta yi dangane da manufarta kan kasar Sin. (Tasallah Yuan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China