Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Binciken Duniyar Mars-Matsoraci Ba Shi Zama Gwani
2020-07-24 15:48:53        cri

A ranar Alhamis 23 ga wata bisa agogon Beijing ne, kasar Sin ta yi nasarar harbar rokar Long March-5, dake dauke da na'urar binciken duniyar Mars mai suna Tianwen-1 da kasar ta kera, kuma irin ta ta farko zuwa sararin samaniya.

Na'urar Tianwen-1, wanda ke da nufin "Tambayar sararin samaniya", ta samo asali ne daga wata dadaddiyar wakar gargajiyar kasar Sin yau shekaru fiye da 2200. Don haka tashinta zuwa duniyar Mars a wannan karo yana dauke da burin dukkan al'ummomin Sin na da da na yanzu game da binciko gaskiya, da zurfafa binciken kimiyya, da gano abubuwan dake kunshe cikin asalin rayuwa, da duniyar bil Adama.

A tarihin dan Adam, an gudanar da ayyukan binciken duniyar Mars fiye da sau 40, kuma an yi nasara a sau 24, wadanda yawancinsu ya shafi ayyukan kewaye da sauka. Ko da yake damar samun nasarar binciken Mars ta kai kimanin kaso 50 cikin dari ne kawai, amma Sinawa masu nazarin sararin samaniya sun nuna jarumtaka tare da zabin wata hanya mafiya wahala. Wato a wannan karo, rokar Long March mai dakon kumbuna ta kai na'urar Tianwen-1 da'irar da ta kewaye duniyar Mars da ta raba kewaye duniyarmu kai tsaye. Haka kuma a wannan karo, ana sa ran na'urar za ta kammala ayyukan kewaya, da sauka, ta kuma yin tafiya a doron duniyar Mars gaba daya. Bugu da kari, a wannan karo, za a yi amfani da na'urorin kimiyya mafiya inganci na zamani guda 13 wajen binciken duniyar Mars daga dukkan fannoni.

Hakika dai, yau shekaru hudu ke nan, tun lokacin da gwamnatin kasar Sin ta amince da shirin binciken duniyar Mars a watan Janairu na shekarar 2016 zuwa samun nasarar harba na'urar Tianwen-1. Lamarin da ya shaida gaskiyar kalaman shugaban kasar Sin Xi Jinping, wato babban sha'ani yana farawa ne daga babban buri, ya kuma ci gaba ne bisa tushen kirkire-kirkire, sa'an nan ya samu nasara ne sakamakon yin aiki tukuru.

Yadda aka harba na'urar Tianwen-1 don binciken duniyar Mars zai taka muhimmiyar rawa a tarihi. Ga kasar Sin, zai zama tamkar wata babbar nasara ce, gaba ga ci gaban sha'anin kimiyya da fasaha na nazarin sararin samaniyarta, matakin da ya bude wa Sinawa wata kofar binciko wata duniya ta daban baya ga duniyarmu. Kana ga duniya, lamarin ya shaida cewa, masu binciken sararin samaniya na kasa da kasa sun kara samun kwarin gwiwa, wanda zai ba da gudummawa wajen taimaka wa bil Adama kara fahimtar abubuwan dake kewaya da duniya.

"Duniya ba ta da iyaka, don haka aikin binciken duniya ba zai tsaya har abada ba. Muddin aka ci gaba da aiwatar da kirkire-kirkire, al'ummar Sin za ta iya samun makoma mai haske." A cewar Shugaba Xi Jinping. Yadda na'urar Tianwen-1 za ta gudanar da bincike a duniyar Mars ya zama mataki na farko mai muhimmanci a fannin bincike na duniya na kasar Sin. Amma bayan kammala wannan aiki mai muhimmanci, za mu iya kara fahimtar abubuwa a zahiri game da duniya, kuma idan muka ci gaba da nacewa, to za mu samu karin alheri, matakin da zai taimaka ga ci gaban bil Adama. (Kande Gao, ma'aikaciyar sashen Hausa na CRI)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China