Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Na'urar Binciken Duniyar Mars Mai Suna Tianwen-1 Za Ta Kawo Wa Dukkan Bil'Adama Alheri
2020-07-23 20:29:19        cri

Yau Alhamis 23 ga wata, kasar Sin ta yi nasarar harba na'urar binciken duniyar Mars ta farko mai suna Tianwen-1, lamarin da ya kasance mataki na farko da kasar Sin ta dauka a fannin binciken taurari. Hadaddiyar daular Larabawa da kasar Amurka sun riga ko suna shirya harba irin wannan na'urar binciken duniyar Mars. Wannan shi ne matakin farko da dam Adam ya kaddamar da shirye-shiryen binciken duniyar Mars guda 3 duka a fili.

Abin lura a nan shi ne a wannan karo, kasar Sin ta harba na'urar binciken duniyar Mars mai suna Tianwen-1 ne domin gudanar da ayyuka guda 3 a lokaci guda, wato harbar na'urar, sannan na'urar za ta kewaya da kuma sauka, sannan za ta yi tafiya a doron duniyar Mars, za kuma ta dauko bayanan zuwa duniyarmu. Wannan babban ci gaba ne da kasar Sin ta samu a tarihin sha'anin binciken sararin samaniya, kuma shi ne karo na farko da aka yi haka a duniya.

Har kullum kasar Sin na nacewa kan yin mu'amala da hadin gwiwa a tsakaninta da sauran kasashen duniya a fannin sararin samaniya, bisa ka'idar mutunta juna da yin adalci da juna, yin amfani da sararin samaniya cikin lumana da kuma neman samun ci gaba da ya kunsi sassa daban daban. A cikin na'urar binciken duniyar Mars mai suna Tianwen-1, akwai wasu injunan nazarin kimiyya daga hukumar samarin samaniya ta Turai, cibiyar nazarin sararin samaniya ta kasar Faransa, da hukumar kara azama kan nazari ta kasar Austria, wadanda za su yi bincike kan duniyar Mars. Sa'an nan kuma kasar Sin ta samu taimako daga kasar Argentina ta fuskar aikin sadarwa a sararin samaniya. Ma iya cewa, yadda na'urar binciken duniyar Mars mai suna Tianwen-1 take gudanar da aikin bincike, ya zama abin koyi ta fannin yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa. Kuma zai kara azama kan raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'Adama. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China