Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Zargin da Pompeo ya yi ba shi da tushe bare makama
2020-07-24 10:42:06        cri

Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi watsi da zargin da sakataren wajen Amurka ya yi, na alakar "cudanni in cude ka" tsakanin kasar Sin da WHO. Mr. Tedros ya kara da cewa, zarge zargen da Pompeo ke yi ba su da tushe bare makama.

Da yake tsokaci yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, babban daraktan WHOn ya ce, nauyin dake wuyan hukumar shi ne kiyaye rayuka, don haka ba wani mutum da zai iya karkatar da hankalin ta daga wannan muhimmin aiki. A hannu guda kuma, yana fatan sauran kasashen duniya ma ba za su bari a kautar da hankalin su daga wannan muhimmin aiki ba.

Mr Tedros ya kara da cewa, siyasantar da batun COVID-19, na ci gaba da zama babbar barazana, duba da cewa cutar ba ta da shinge, ba ta san wani banbancin ra'ayi ko jam'iyyar siyasa ba.

An rawaito cewa, yayin wani taro tsakanin Mr. Pompeo da rukunin wasu 'yan majalissar dokokin Birtaniya da ya gudana a ranar Talata, Pompeo ya yi zargin cewa, akwai wasu shaidu da ke nuna yadda aka yiwa Mr. Tedros alfarmar darewa jagorancin hukumar WHO, matakin da a cewar sa, ya haifar da mutuwar 'yan Birtaniya da dama sakamakon yaduwar cutar COVID-19.

Har wa yau a dai taron na jiya Alhamis, babban daraktan sashen ayyukan gaggawa a hukumar WHO Mike Ryan, ya ce yana matukar goyon bayan jagorancin Mr. Tedros, duba da irin nagartar ayyukan da yake jagoranta.

Ita ma Maria Van Kerkhove, Ba'amurkiya, kuma shugabar fasaha ta sashin ayyukan gaggawa a hukumar, ta ce ita shaida ce game da kwazon Dr. Tedros, don haka ba za su amince wani ya karkatar da hankalin su daga managartan ayyukan da suke gudanarwa karkashin hukumar ta WHO ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China