Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masani dan Birtaniya: tabbatar da ikon WHO abu ne mai muhimmanci
2020-07-13 10:50:24        cri

Jiya Lahadi Aftab Siddiqui, dan Birtaniya, mai sharhi kan harkokin kasashen waje, ya bayyana matakin Amurka na ficewa daga hukumar lafiya ta duniya WHO, a matsayin abun kunya da bakin ciki. Yana mai jaddada cewa, tabbatar da ikon WHO abu ne mai matukar muhimmanci, don haka, dole ne kasashen duniya su hada hannu wajen yaki da annobar COVID-19.

Farfesa Aftab Siddiqui ya bayyana cewa, matakin na Amurka sam bai dace ba, a lokacin da annobar ta dabaibaye kasar. Ya ce bisa la'akari da yanayin da ake ciki na yaki da annobar, lokaci ne da ya dace a karfafa hadin gwiwa don shawo kan matsaloli tare. Babu wata kasa da za ta iya cin nasara ita kadai.

Ya ce hukumar WHO na taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar duniya ta fuskar tunkarar matsalolin lafiya, don haka, tabbatar da ikonta muhimmin abu ne a lokacin da ake yaki da annoba.

Farfesa Siddiqui, ya kuma yi kira ga dukkan kasashe su shirya cike gibin da Amurka ta bari tare da hada hannu wajen gaggauta yaki da annobar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China