Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen duniya sun yi tir da janyewar Amurka daga WHO
2020-07-10 11:31:24        cri

Yayin da yawan masu harbuwa da annobar cutar numfashi ta COVID-19 yake ta karuwa a cikin gidan kasar, gwamnatin kasar Amurka ta kaddamar da aniyarta na ficewa daga hukumar lafiya ta duniya wato WHO a hukumance, lamarin da ya jawo mata suka daga kasashen duniya. Janyewar Amurka daga WHO ba kawai zai illata kokarin da take yi na yaki da annobar ba ne, har ma zai kawo illa ga hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da annobar.

Dangane da lamarin, Richard Horton, babban edita na shahararriyar mujallar The Lancet ta fannin ilmin likitanci ya rubuta wani bayani dake nuna cewa, janyewar Amurka daga WHO zai lahanta tsaron kanta, da kuma tasirin da take takawa ta fuskar diplomasiyya, haka kuma zai kawo illa ga ayyukan WHO, musamman ma yin nazari kan allurar rigakafin annobar ta COVID-19. Wadannan ayyuka na bukatar hadin gwiwar kasa da kasa, wadanda kuma kasashen duniya za su ci gajiya. Kasashen duniya na bukatar inganta hadin kai da WHO wajen tabbatar da tsaron lafiyar al'ummomin kasa da kasa.

Madam Maria Zakharova, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta sanar a ranar 9 ga wata cewa, Rasha ta ki yarda da sanya siyasa kan batun hadin gwiwar kasa da kasa ta fuskar kiwon lafiya. A cewarta, matakin da Amurka ta dauka ba shi da amfani. Kamata ya yi WHO ta ci gaba da bada jagora da taimako wajen hadin kan duniya ta fuskar kiwon lafiya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China