Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bukatar rufe ofishin jakadancin Sin dake Houston takala ce irin ta siyasa
2020-07-23 09:51:21        cri

Babban ofishin jakadancin kasar Sin a Amurka, ya ce bukatar da mahukuntan Amurka suka mika na rufe karamin ofishin jakadancin Sin dake birnin Houston takala ce irin ta siyasa, kuma mataki ne maras dacewa, da ka iya kara lahanta dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.

Wata sanarwa da babban ofishin jakadancin na Sin ta fitar a jiya Laraba, ta ce ba zato ba tsammani, gwamnatin Amurka ta bukaci dakatar da dukkanin ayyukan da ofishin na Houston ke gudanarwa cikin wani kankanin wa'adi, wanda hakan ya yi matukar sabawa dokokin kasa da kasa, ya kuma yi karan tsaye ga ka'idojin cudanyar kasa da kasa, da ma yarjejeniyar da sassan biyu suka amincewa a fannin ayyukan diflomasiyya.

Bangaren Sin dai ya yi matukar Allah wadai da wannan mataki, kasancewar har kullum, Sin na iya kokarin ta wajen martaba ka'idar rashin tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashen duniya.

A duk tsawon shekarar nan ta bana, ofisoshin jakadancin Sin dake Amurka ciki hadda na birnin Houston, na gudanar da ayyukan su yadda ya kamata, bisa tanajin yarjejeniyar Vienna mai nasaba da cudanyar diflomasiyya, da burin kyautata yarjejeniyar dake tsakanin Sin da Amurka, da musaya da hadin gwiwa, tare da fadada fahimtar juna, da kawance tsakanin al'ummun sassan biyu.

Sanarwar ta kara da cewa, dukkanin zarge zargen da Amurka ke yi wa Sin ba su da tushe ko makama, sai dai idan har burin Amurka bai wuce tsangwamar kasar Sin ba, to kuwa har kullum ba za ta gaji da zakulo dalilai marasa tushe na yin hakan ba.

Daga nan sai sanarwar ta yi kira ga Amurka, da ta gaggauta janye wannan mataki na kuskure da take burin aiwatarwa. Tana mai cewa, gaza yin hakan zai jawo Sin ta maida martanin da ya wajaba bisa doka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China