Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi da Trump za su hau matakin farko na sulhunta takaddamar ciniki
2019-07-04 15:39:24        cri

Yayin da kasashen Sin da Amurka suka shiga yakin ciniki, ana sa ran matsayar da shugabannin kasashen biyu za su cimma za ta ci gaba kuma ana fatan za'a cimma matakin farko game da ci gaban yarjejeniyar a nan gaba, wani kwararren masanin harkokin kasuwanci ne ya bayyana hakan.

"Sake komawa teburin sulhun, wani mataki a yunkurin da ake na neman cimma matsaya, wanda idan aka ci gaba da ginawa sannu a hankali, ana fatan a nan gaba za'a samu muhimmin ci gaba wanda zai amfanawa ci gaban tattalin arzikin kasashen biyu, kuma zai samar da kyakkyawar makoma a nan gaba," in ji Carla A. Hills, babban jami'in kamfanin Hills & Company, dake da sansaninsa a birnin Washington, kamfani ne dake samar da shawarwari game da harkokin ciniki da zuba jari.

A gefen taron kasashen G20 a birnin Osaka na kasar Japan a ranar Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka, Donald Trump, sun amince cewa, bangarorin biyu za su ci gaba da tuntubar juna game da batun tattalin arziki da cinikayya, kuma Amurka ba za ta kara saka harajin kwastam kan kayayyakin kasar ba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China