Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ba za ta rufe kofarta ba
2019-09-25 14:48:03        cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya ce kasar ba za ta rufe kofarta ba, sai dai ma ta kara fadada bude ta.

Wang Yi ya bayyana a wajen liyafar da kwamitin tattauna huldar kasuwanci tsakanin Sin da Amurka da majalisar kula da harkokin kasuwanci tsakanin Sin da Amurka da cibiyar bunkasa cinikayya na Amurka da majalisar kula da harkokin wajen kasar suka shirya cewa, bude kofa, manufa ce ta kasar Sin, kuma kasar ba za ta rufe kofarta ba, wadda sai dai ma ta kara fadada.

Wang Yi, ya ce tun a shekarar 2010, kasar Sin ta cika alkawarin rage haraji da ta yi lokacin da za ta shiga kungiyar WTO, kuma a yanzu, matsakaicin matakin harajinta ya tsaya ne kan kaso 7.5, wanda ya yi kasa da na galibin kasashe masu tasowa.

Ya kara da cewa, kasar Sin na kara gaggauta manufarta ta gyare-gyare a cikin gida.

Har ila yau, Wang Yi ya ce, ana ci gaba da bitar bangarorin da baki ba za su iya zuba jari ba, da kuma tabbatar da adalci da ba su dama iri guda da 'yan kasuwar kasar, inda ya ce, bangarorin da aka takaita musu zuba jari na ci gaba da raguwa a kowacce shekara. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China