![]() |
|
2020-07-20 20:32:24 cri |
Kalaman Wang na zuwa ne, bayan da aka ruwaito sakataren tsaron Amurka Mark Esper a baya-bayan nan na cewa, babbar abokiyar takarar Amurka ita ce kasar Sin, sai Rasha, amma kasar Sin tana da babbar matsala. Da yake amsa tambayoyin manema labarai kan wannan batu, Wang ya yi nuni da cewa, har kullum kasar Sin tana martaba ka'idojin kasa da kasa da yin kira da ma nuna adalci da daidaito a harkokin kasa da kasa, sabanin yadda Amurka ta sha janyewa daga yarjejeniyoyi na kasa da kasa da ma nesanta kanta daga harkokin da suka shafi al'ummomin duniya.
A don haka, kasar Sin tana kira ga Amurka, da ta yi watsi da ra'ayin yakin cacar baka, ta daina furta kalamai da aikata abubuwan da ba su dace ba, ta hada kai da kasar Sin, don dawo da alakar kasashen biyu bisa turbar da ta dace ta daidaito, da hadin gwiwa da kwanciyar hankali. (Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China