Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kayayyakin tsaron da aka kafa a masallacin birnin Kashgar na jihar Xinjiang sun kare tsaron musulmai
2020-07-18 17:27:37        cri

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, 'yan ta'adda da 'yan aware da masu tsattsauren ra'ayin addini sun aikata laifuffukan da suka kai ga kashe mabiya addini da dama, alal misali a ranar 30 ga watan Yulin shekarar 2014, 'yan ta'adda guda uku sun kashe mataimakin shugaban kungiyar addinin musulmi ta jihar Xinjiang mai shekaru 74.

Domin tabbatar da tsaron musulmai, an kafa wasu kayayyakin kare rayuka a wasu masallatai dake birnin Kashgar, matakin da ya samu karbuwa matuka daga musulmai a birnin, amma rahoto kan 'yancin addini na kasa da kasa na shekarar 2019 da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar ya bayyana cewa, an kafa kayayyakin ne domin sa ido kan ibadun musulmai.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China