Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A karon farko, jimilar kudin kayayyakin ciniki na shigi da fici da Sin ta samu ta karu a bana
2020-07-15 11:03:28        cri

Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar da alkaluma a jiya Talata, inda aka nuna cewa, a tsakanin watan Janairu zuwa Yunin bana, jimillar kudin cinikayyar shigi da fici da kasar ta samu ya kai kudin Sin RMB yuan triliyan 14.24, adadin da ya ragu da kashi 3.2 cikin 100 bisa na makamancin lokacin bara. Kana a watan Yuni, jimilar kayayakin da kasar ta fitar ta karu da kashi 4.3 cikin 100, yayin da yawan kayayyakin da aka shigo da su ya karu da kashi 6.2 cikin 100, wannan shi ne karon farko da aka samu wannan karuwa a shekarar da muke ciki, farfadowar cinikin waje da aka samu ta wuce hasashen da aka yi.

 

 

A yayin taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar a jiya Talata, kakakin babbar hukumar kwastam ta kasar, kuma shugaban sashen kididdiga da nazari Li Kuiwen ya bayyana cewa,

"A cikin manyan abokan cinikayyarmu guda goma, wadanda suka samu karuwar cinikayyar waje tare da Sin a watanni shida na farkon bana, sun kai biyar, amma a tsakanin watan Afrilu da Yuni, sun kai takwas. A cikinsu, kasashe mambobin kungiyar ASEAN ta fi nuna fifiko a wannan fannin, sakamakon hali mai kyau da yankin ke ciki wajen dakile yaduwar annobar COVID-19, ban da wannan kuma, a 'yan shekarun nan, kungiyar karfafa hadin kai tare da Sin a fannonin tattalin arziki da cinikayya, ta inganta tsarin sana'o'i a tsakanin bangarorin biyu, ta yadda za a samu karuwar cinikayya a tsakaninsu. A watanni shida na farkon bana, jimillar kudin kayayyakin cinikayya da aka samu a tsakanin kasar Sin da kasashen ASEAN ta kai RMB triliyan 2.09, wato ta karu da kashi 5.6 cikin 100 bisa na makamancin lokacin bara, adadin da ya kai kashi 14.7 cikin 100 bisa na daukacin jimilar cinikayyar kayayyakin kasar ta Sin, wanda ya karu da kashi 1.2 cikin 100 bisa na makamancin lokacin bara."

 

 

Alkaluman da hukumar kwastam ta fitar na nuna cewa, kasar Sin ta samu saurin karuwa a fannin fitar da kayayyakin da suka shafi dakile annobar COVID-19, da kuma kayayyakin gudanar da aiki da sayar da kayayyaki a cikin gida. A farkon rabin shekarar bana, yawan kayayyakin saka da kasar ta fitar, ciki har da abubuwan rufe baki da hanci ya karu da kashi 32.4 cikin 100, sauran kayayyaki kamar magunguna da kayayyakin sarrafa magunguna, da na'urorin aikin jinya, sun kai kashi 23.6 cikin 100 da kashi 46.4 cikin 100. Karuwar kayayyakin gudanar da aiki da aka sayar, da sayen kayayyaki a cikin gida ta inganta karuwar fitar da kananan kamfuta sanfurim Nap-top da ta kai kashi 9.1 cikin 100, da ta wayar salula kashi 0.2 cikin 100.

Baya ga haka kuma, masana'antu da ba na gwamnati ba su ma sun samu bunkasuwa a fannin shigi da ficin cinikayyar waje. A farkon rabin shekarar bana, a matsayin ginshiki na farko na cinikayyar waje, darajar kayayyakin da masana'antun da ba na gwamnati ba suka fitar ta kai RMB triliyan 6.42, wanda ya karu da kashi 4.9 cikin kashi 100.

Kakakin babbar hukumar kwastam ta kasar Sin Li Kuiwen ya bayyana cewa, yanzu ana samun babban sauyi sakamakon yaduwar annobar, tattalin arzikin duniya na fuskantar koma baya sosai, kana ana samun raguwar cinikayyar kasa da kasa da zuba jari a ketare, hakan ya sa kasar Sin take fuskantar yanayi mai sarkakiya na samu ci gaban cinikayyar waje. Ya ce,

"Kasar Sin na kara fuskantar rashin tabbas da daidaito wajen neman bunkasuwar cinikayyar waje, a karshen rabin shekarar bana, za ta ci gaba da fuskantar yanayi mai tsanani na shigi da fici. Amma, duk da haka mun gano cewa, kasar Sin yana da karfin tinkarar duk wani hadari da ka iya kunno kai. Bisa jerin matakan da aka kaddamar game da tabbatar da cinikayyar waje, muna cike da imani kan ba da tabbaci ga babban tushen cinikayyar waje, da nufin inganta zaman karko da kara ingancin shigi da ficin kayayyaki."

 

 

Game da halin da za a fuskanta a fannin cinikayyar waje a karshen rabin shekarar bana, babbar cibiyar nazarin harkokin kudi ta bankin BCM na kasar Sin Tang Jianwei yana ganin cewa, idan aka dakile yaduwar annobar Covid-19 a duk fadin duniya, to ana sa ran cinikayyar waje ta kasar Sin za ta ci gaba da farfadowa. Ya bayyana cewa,

"Kwanan nan, ana ta samun kyautatuwar yanayin annobar a yankin Turai, hakan ya taimaka wajen soma farfado da tattalin arzikin Turai da Amurka, don haka, ana tunanin za a samu farfadowar bukatun waje sannu a hankali. A waje guda kuma ana samun farfadowar bukatu a cikin gida, yanzu ana samun kyautatuwar sayen kayayyaki a cikin gida, da inganta shigo da kayayyakin masarufi. Bisa hasashen da aka yi, an ce, yanayin shigo da kayayyaki zai fi yadda ake fitar da kayayyakin, mai yiwuwa rarar kudin cinikayyar waje za ta ragu." (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China