Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin kasar Sin ta samar da kudin tallafi ga Zimbabwe don sake gina wani yankin da bala'in guguwa ta shafa
2020-07-04 16:49:07        cri
An kaddamar da wani aikin tallafawa yankin da bala'in guguwa ya shafa a birnin Harare, fadar mulkin kasar Zimbabwe, a jiya Juma'a. Gwamnatin kasar Sin ce ta samar da kudin gudanar da wannan aiki, yayin da hukumar raya kasashe ta MDD, wato UNDP, ke kula da aiwatar da shi.

Karkashin wannan aiki, ana sa ran samar da sabbin gidaje 237, da kananan asibitoci 8, da wasu makarantu, da gyaran wasu makarantu da asibitoci, a yankunan dake gabashin kasar Zimbabwe, inda mahaukaciyar guguwar da ake kira Idai ta shafa.

A cewar hukumar abinci ta duniya WFP, bala'in guguwar ya haddasa asarar rayuka a kalla 185, da raba wasu fiye da dubu 10 da matsugunansu a kasar Zimbabwe, inda mutane dubu 270 ke bukatar dauki cikin gaggawa.

A wajen bikin kaddamar da shirin ginin, jakadan kasar Sin dake Zimbabwe, mista Guo Shaochun ya ce, kasar Sin da kasar Zimbabwe kawaye ne da ke da huldar hadin kai da ta shafi manyan tsare-tsare. Don haka a lokacin da ake fuskantar mawuyacin hali, kasashen za su yi kokarin taimakawa juna don neman daidaita matsalolin da ake fuskanta cikin sauri. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China